CDU ta sake zabar Merkel a matsayin shugaba | Siyasa | DW | 07.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

CDU ta sake zabar Merkel a matsayin shugaba

Wakilan jam'iyar CDU sun sake zabar Angela Merkel a matsayin jagorar jam'iyyar a karo na tara, abinda ke nunan tabbacin shugabar gwamnatin za ta ci gaba da shirinta na yunkurin yin ta-zarce a zaben kasar da ke tafe.

Essen CDU-Bundesparteitag t
Essen CDU Bundesparteitag Abstimmung Tauber Merkel Kauder (picture-alliance/dpa/M. Kappeler)

CDU ta sake zabar Merkel a matsayin shugaba

To wannan dai wata gagarumar nasara ce ga Angela Merkel wacce a yanzu batun 'yan gudun hijira ke neman kawo mata bakin jini. To amma duk da cewa batun na karbar baki da ke zama babbar muhawara a Jamus, inda har ta kai ga jam'iyyar CDU ta fadi a wasu zabukan jihohi da kananan hukumomi, sai dai idan aka yi la'akari da yawan kuri'un da Merkel ta samu za a iya cewa har yanzu tana shugabar gwamnatin Jamus din na da matukar farin jini a cikin jam'iyyar tata. A takaice dai kashi goma ne cikin dari na wakilai suka ki amince wa da Merkel kuma haka tabbas ya nuna farinjininta na nan a jam'iyyar da take shugabanta har karo na  tara. Ba tare da bata lokaci Merkel ta bayyanan manyan matsalolin da a yanzu ke gabanta, inda ta ce:

"Idan aka yi la'akari da harin da aka kai a Faransa da tangal-tangal da yarjejeniyar tsagaita wuta a fadan Ukraine da matsalolin basussuka a kasar Girka da kuma bakin da ke tuttudowa zuwa Turai, hasali ma cikin kasar Jamus don samun mafaka, musamman 'yan gudun hijira daga Afghanistan da Iraki da Siriya da kuma 'yan kasashen Afirka, ba wai dukkan wadannan mutanen ne za su zauna cikin kasarmu ba, kuma da dai-dai sai an binciki ko wannensu."

Suma dai 'yan jam'iyar ta CDU sun tabka muhawara akan batun shigowar baki, wanda kusan shi ne ya mamaye taron da wakilan suka halarta kuma su kansu sun nemi shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta sauya.

Bisa wannan zaben dai Angela Merkel za ta jagoranci jam'iyyar CDU na tsawon shekaru biyu nan gaba, kamar yadda wa'adin yake a karkashin ka'idojin jam'iyyar ta CDU.

Sauti da bidiyo akan labarin