CDU da FDP sun lashe zaɓen ´yan majalisar dokokin jihar Hesse | Siyasa | DW | 19.01.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

CDU da FDP sun lashe zaɓen ´yan majalisar dokokin jihar Hesse

Ba a yi mamakin sakamakon zaɓen ´yan majalisar dokokin jihar Hesse dake nan Jamus wanda aka gudanar a ranar Lahadi ba.

default

Roland Koch Firimiyan Jihar Hesse

A haɗe jam´iyun CDU da FDP sun samu gagarumin rinjaye kuma za su ci-gaba da wannan ƙawance har bayan zaɓen ´yan majalisar dokokin tarayya a ƙarshen wannan shekara.

Firimiyan jihar Hesse Roland Koch zai ci-gaba da mulki bayan da jam´iyarsa ta CDU ta samu kashi 37 cikin 100 na yawan ƙuri´u wato fiye da sauran jam´iyu da suka tsaya takara a zaɓen. Tare da ƙawarta jam´iyar FDP, sun samu gagarumin rinjaye ta yadda za su iya kafa gwamnati. Roland Koch wanda ya ɗare kan muƙamin Firimiyan jihar ta Hesse tun a 1999 ya nuna farin cikinsa game da sakamakon zaɓen.

"Yanzu dai ya tabbata cewa CDU da FDP sun samu rinjayen ƙuri´u a wannan jiha ba kamar yadda ya kasance a fagen siyasarmu na rashin samun rinjaye ba. Wannan wata riba ce ga jihar Hesse baki ɗaya."

To sai dai bai kamata wannan murna ta sa a manta cewa CDU ba ta samu ƙarin ƙuri´u ba idan aka kwatanta da zaɓen da ya gudana a jihar kimanin shekara guda da ta gabata. Ita kuwa FDP ta ci gajiyar dambarwar siyasar da aka yi fama da ita a tsawon shekara guda, inda a wannan zaɓe ta samu kashi 16 cikin 100 wato adadi mafi yawa a Hesse tun bayan shekarar 1954 kana kuma ta samarwa CDU rinjaye a majalisar dokokin jiha. Shugaban FDP Guido Westerwelle ya bayyana wannan sakamakon da cewa zai kawo ƙarshen babban ƙawance a gwamnatin tarayya.

"Wannan babbar rana ce ga jihar Hesse kuma kyakkyawan mafari ne ga Jamus musamman dangane da jerin zaɓuɓɓuka da za a gudanar a ƙasar cikin wannan shekara."

Ga SPD kuwa zaɓen bai zo mata da kyau ba domin ta samu kashi 24 cikin 100 wato ta yi asarar ƙuri´u kimanin kashi 13 cikin 100 idan aka kwatanta da yawan ƙuri´un da ta samu a bara. Shugabarta Andrea Ypsilanti ta gaza kafa gwamnati a bara saboda haka aka yi waje da ita.

"Jam´iyar SPD a Hesse ta kwashi kashinta a hannu. Wani ɓangare na masu kaɗa ƙuri´a ba su yafe mana ba saboda kasa samun rijnyaje a watan Nuwamban bara don sauyin gwamnati. Sannan ɗaya ɓangaren kuma ba su ji daɗin yadda muka so kafa wata gwamnati maras rinjaye ba."

Ypsilanti ta ɗauki alhakin wannan kaye da jam´iyar ta sha a saboda haka ta sauka daga muƙamin shugabar SPD a jihar ta Hesse. Yanzu haka dai an naɗa ɗan takararta a zaɓen Thorsten Schäfer-Gümbel don ya maye gurbinta. Hatta shi kanshi shugaban SPD Franz Müntefering ya yi magana game da mummunan sakamako ga jam´iyarsa a Hesse, amma ya ce haka ba zai zama manuniya ga zaɓen ´yan majalisar dokokin tarayyar da zai gudana a cikin watan Satumba mai zuwa ba.

Yayin da SPD ta faɗi ita kuwa jam´iyar The Greens ƙarin ƙuri´u ta samu a jihar ta Hesse inda ta samu kashi 14 cikin 100 wato ƙuri´u mafi yawa da ta taɓa a samu a wani zaɓen majalisun jihohi.

CDU da FDP a Hesse za su gaggauta cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin ƙawance. Yanzu haka dai akwai irin wannan ƙawance tsakaninsu a jihohi biyar na Jamus. Yayin da CDU ke ganin zaɓen na Hesse a matsayin wani kyakyawan mafari ita kuwa SPD fata take cewa sakamakon zaɓen zai tsaya ne a jiha kaɗai.