Canza akalar kuɗin taimako a Habasha | Zamantakewa | DW | 09.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Canza akalar kuɗin taimako a Habasha

Ana zargin canza akalar kuɗeɗen taimako ga masu fama da matsalar yunwa a Habasha shekarun 1980, inda 'yan tawaye suka yi amfani da su don sayen makamai

default

Mtsalar yunwa ta addabi ƙasar Habasha a shekarun 1980

Rahotanni sun nuna cewar an juya kuɗaɗen taimakon da aka gabatarwa da ƙasar Habasha domin tinkarar matsalar yunwar da ta addabi ƙasar a cikin shekarun 1980 domin sarrafa su ta wasu hanyoyi daban. Kimanin kwatankwacin Euro miliyan 100 aka tara a wani bikin kiɗan da aka shirya don neman kuɗaɗen taimako ga ƙasar ta Habasha a shekara ta 1985. Amma waɗannan kuɗaɗe sun kwarara ne zuwa baitul-malin wata ƙungiyar dake fafutukar kifar da tsofuwar gwamnati ta Mengitu Haile Mariam, inda tayi amfani da su wajen sayen makamai.

Tun dai a wajejen tsakiyar shekarun 1980 ne hukumar leƙen asirin Amirka ta CIA ta ba da rahoton cewar bisa ga dukkannin alamu maƙudan kuɗin da aka tura domin sassauta raɗaɗin yunwar da jama'a ke fama da ita a arewacin ƙasar Habasha sun kwarar zuwa baitul-malin ƙungiyar tawayen Tigray ta TPLF domin amfani da su wajen sayen makamai. A wancan lokaci gwamnatin makisanci ta Mengistu Haile Mariam tana fafatawa da ƙungiyoyin tawaye daban-daban, abin da ya haɗa har da TPLF ta Meles Zenawi, shugaban ƙasar Habsha na yanzu. Yau kimanin shekaru 25 bayan haka jita-jita ta ƙara tabbatuwa sakamakon bayanin da aka ji daga wani kwamandan 'yan tawayen da a yanzu haka yake zaman hijira a ƙasar Netherlands. A lokacin da gidan rediyan DW ya tuntuɓe shi, Dr. Aregawi Berhe yayi bayani a game da aka samu kafar yaudarar ƙasashen dake da hannu a taimakon inda yake cewar:

"Kafofin ba da lamuni sun gabatar da kuɗeɗen ne tare da fatan cewar zasu amfanar da ɗimbim mutanen dake buƙatar taimako. Ƙungiyar tawaye ta TPFL ta karɓi kuɗin bisa iƙirarin cewar zata danƙa wa wata ƙungiya ce mai fafutukar raya makomar Tigray, MARET a taƙaice don raba wa mabuƙata. Amma fa MARET na ba da cikakken goyan-baya ɗari-bisa-ɗari ga ƙungiyar tawayen. Bayan tara kuɗaɗen daga kafofi daban-daban dake ba da lamuni, ƙungiyar ta taimakon ta shigar da su a kasafin kuɗin kwamitin zartaswa ta TPFL domin aiwatar da su a fafutukarta ta kifar da gwamnati."

Ita dai TPLF, ita ce ginshiƙin ƙungiyoyin tawayen dake haɗin guiwa ƙarƙashin tutar ƙungiyar juyin-juya-halin demoƙraɗiyya ta al'umar Habasha EPRDF ta shugaba Mlese Zenawi dake mulkar ƙasar Habasha tun abin da ya kama daga 1991. Tuni dai kakakinta Sekuture Getachew ya musunta wannan zargi:

"Ka da fa mu manta cewar ƙungiyar TPLF a wancan lokaci ta gabatar da roƙon taimako ga ƙasashe masu ba da lamuni don su kai taimako ga dubban ɗaruruwan mutanen dake fuskantar barazanar yunwa a lardin Tigray. Kuma ƙungiyar EPRDF mai mulki, wadda kuma TPLF ke ƙarƙashin tutarta tayi shekara da shekaru tana da kyakkyawan suna tsakanin ƙasashe dangane da yadda take amfani da kuɗaɗen taimakon ta hanyar da ta dace. Mutanen dake neman shafa mana kashin kaza a yanzun, ba kowa ba ne illa waɗanda suka fice daga ƙungiyar saboda wasdu dalilai na ƙyashi."

Ita ma ƙungiyar Christian Aid ta Birtaniya dake da hannu a taimakon na 1984 da 1985 ta ce ba ta da wata alaƙa da zargin da ake yi na amfani da kuɗin ta hanyar da ba ta dace ba. Su dai tsaffin 'ya'yan ƙungiyar su biyu dake ba da shaidar wannan zargi Aregawi da Gebremedhin, tun da jimawa suka yi hannun riga da Meles Zenawi suka kuma yi ƙaura domin zaman hijira a ƙetare. Kuma gabatar da waɗannan bayanan watanni uku gabanin zaɓen Habasha, ba shakka wani yunƙuri ne da adawa da jami'yyar dake mulki.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita:Abdullahi Tanko Bala