1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Canjin yanayi na illa ga rayuwar yara

Gazali Abdou TasawaNovember 24, 2015

Sakamakon bincike da Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ta wallafa ya nuna cewa canjin yanayi da duniya ke fiskanta na yin illa ga rayuwar yara miliyan 690 a duniya.

https://p.dw.com/p/1HB2y
Kinder in Sierra Leone
Hoto: UNICEF

Rahoton Asusun na Unicef ya nunar da cewa yara kimanin miliyon 530 na rayuwa ne a kasashen da ke fama da matsalar ambaliya akasarinsu a nahiyar Asiya, a yayin da wasu miliyon 160 ke rayuwa a yankunan da ke fama da matsalar fari musamman a nahiyar Afirka.

Unicef wacce ta bayyana sakamakon wannan bincike nata a lokacin da ya rage 'yan kwanaki a gudanar da babban taron muhalli na duniya a birnin Paris ta ce karuwar zafin rana da mahaukacciyar guguwa da dai sauran bala'o'i da ke da nasaba da sauyin yanayi na taimakawa wajen yaduwar cututuka irinsu maleriya da tamowa da gudawa da dai sauran cututtuka masu saurin kisan yara.