1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cameron: Birtaniya ba za ta juya wa EU baya ba

Yusuf BalaJune 27, 2016

A cewar Cameron dai wannan mataki na ficewa daga EU abu ne mai wahala kasar ta dauka amma dole ta jure duk wani nau'i na kalubale.

https://p.dw.com/p/1JEc6
Symbolbild EU Krise
Hoto: Getty Images/C. Furlong

Firaministan Birtaniya David Cameron ya fada wa 'yan majalisar dokoki a Birtaniya cewa duk da kasancewar kasar ta zabi ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai wannan baya nuna cewa za ta juya baya ga kungiyar ko ma wani yanki na duniya. A cewar Cameron dai wannan mataki ne mai wahala kasar ta dauka amma dole ta jure duk wani nau'i na kalubale da za ta iya fiskanta.

Ya ce "Dole mu samu karfin gwiwa cewa Birtaniya ta shirya ta tunkari duk irin kalubale da ke gabanta, ko da yake kasarmu ta kasance daya cikin masu karfi a fannin tattalin arziki a duniya, mun shirya tukarar kalubale da ke gabanmu."

Cameron ya kuma yi Allah wadai da halayyar da wasu 'yan kasar suka nunar ta nuna kin jinin baki bayan da aka bayyana sakamakon kuri'ar raba gardamar.

Ya ce zai bar wanda zai gaje shi da tunkarar sabuwar dangantakar Birtaniya da kungiyar ta kasashen Turai. Tuni dai yankin Scotland ya bayyana aniya ta neman hadin kan 'yan majalisar yankin a kokari na sake hada kai da kungiyar ta EU.