Cafke yan Tarzoma a jamus | Siyasa | DW | 05.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Cafke yan Tarzoma a jamus

A jiya ne jamian yan sanda suka cafke yan tarzoma guda uku

Yan Tarzoma da aka cafke a Jamus

Yan Tarzoma da aka cafke a Jamus

Jamian tsaro a nan tarayyar jamus sun cimma nasarar kare aiwatar da manyan hare haren boma bomai da wasu yan tarzoma guda uku suka shirya kaiwa a wurare daban daban guda biyu dca suka hadar da filin saukan jiragen sama na birnin Frankfurt da kuma headquatan sansanin dakarun Amurka na turai dake nan tarayyar jamus.

Mai gabatar da kara a madadain gwamnatin Monika Harms ta bayyanawa manema labaru cewa yan tarzoman uku da suka hadar da jamusawa guda biyu da suka musulunta da mutumin turkiyya,wadanda shekarunsu ke tsakanin 20 zuwa 30 dai,tun cikin watanni shida da suka gabata ne, jamian yansanda kimanin 300 suke lura da harkokin da suke gudanarwa.

Tace yan samu yan tarzoman dauke da kimanin kg 730 na sinadarin Hydrogen,wadanda zaa iya amfani dashi wajen kera boma bomai,makamancin wadanda aka kai hari dasu a a watan yulin shekara ta 2005 a birnin London din kasar Britania.

“tace acikin wani yunkuri guda,Jamian tsaro da hukumomin shigar da kara na gwamnati a nan tarayyar jamus sun cimma gagarumar nasara,inda suka gano wannan shiri na kai hare haren taaddanci alokacin daya dace,kuma cikin kiftawar idanu suka dakatar dashi,wanda sun cimma nasarar aiwatarwa zai zame wani babban balai kamar wanda ya ritsa da harkokin sufuri a abirnin Madrid a shekarata 2004,kuma shekara guda bayan nan ya auku a birnin London.A wadannan hare haren dai sama da mutane dari suka rasa rayukansu”

Shugaban sashin yansanda dake kula da miyagun laifuffuka na nan tarayyar jamus,Jörg Ziercke ya bayyana cewa a halin da ake ciki yanzu,ya dada tabbatar dacewa wannan kasa na fuskantar barazanar ya tarzoma na ketare,batu dake nuni dacewa ayanzu babu cikakken kwanciyar hankali kamar yadda aka sanai a baya.

“A wannan yanayi na barazanar yan tarzoma,muna da jamian yansanda wanda ya zamanto dole su san asalin wadanda suke sansanoni na horaswan kungiyoyin muslimi yan jihadi dake arewacin Pakistan,musamman wadanda keda horan yadda zasuyi amfani da sinadran kai hare hare”

Ministan kula da harkokin cikin gida na jamus Wolfgan Schäuble,yace an cimma nasarar cafke wadannan yan tarzoman ne da taimako tsakanin jamian tsaron Amurka dana jamus.

“Alummomi baki daya zasu iya bada gaskiyar cewa,hukumomi da jamian tsaro,a fadin kasannan suna iyakar kokarinsu wajen tabbatar da tsaron lafiyan jamaa.Adangane da hakane ya zamanto wajibi,wa kowane mutun ya cigaba da gudanar da rayuwarsa ta yau da kullun,ba tare da wata fargaba ba”

A yan makonnin baya nedai Ministan harkokin cikin gidan na jamus yayi gargadi adangane da kasancewar cikin shirin kota kwana adangane da barazanar yan tarzoma.

Duk dacewa majiyar jamian tsaro na nuni dacewa yan tarzoman uku suna shirin afkawa babban filöin jirgin saman birnin Frankfurt ne da kuma headquatar dakarun sojin Amurka dake birnin Ramstein,kakakin rundunar Amurkan dake nan turai Jefferey Gradeck,yace basu da tabbacin cewa sansaninsu ne aka nufa da wannan hari.