1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

CAF: Sheikh Salman ne dan takanmu a FIFA

Mouhamadou Awal BalarabeFebruary 5, 2016

Daukacin membobin kwamitin zartasawa na CAF sun amince da Sheikh Salman al Khalifa a matsayin dan takara da ya cancaci samun karbuwa a zaben shugabancin FIFA.

https://p.dw.com/p/1HqbJ
Bahrain FIFA Sheikh Salman bin Ebrahim Al Khalifa
Hoto: picture-alliance/AP Photo/H. Jamali

Hukumar Kwallon Kafa ta Kasashen Afirka ta zabi Sheikh Salman na kasar Baharein a matsayin dan takarar da za ta mara wa baya a zaben shugaban FIFA da zai gudana a karshen watan Febireru. Mataimakin shugaban CAF Almany Kabele Camara ne ya yi wannan sanarwa bayan da kwamitin zartaswa na Hukumar Kwallon Kafa ta Kasashen Afirka ya yi zamansa a birnin Kigali na kasar Ruwanda.

Wannan goyon bayan da Sheikh Salman ya samu daga CAF ya sanyashi a sahun wadanda za su iya zama shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya na gaba. Ita dai nahiyar Afirka ta fi kowa yawan kuri'a a zaben na FIFA inda za ta tashi da 53. Nahiyar Turai na biya mata baya da kuri'i 53 yayin da Asiya na da 46.

Hudu daga cikin 'yan takara da ke zawarcin kujerar shugabanci FIFA sun hallara a birnin na Kigali domin zawarcin kuri'un 'yan Afirka ciki kuwa harda Sheikh Salman da Gianni Infantino, da Jerome Champagne da Tokyo Sexwale na Afirka ta Kudu.