1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cacar baka tsakanin gwamnatin Erythrea da majalisar Dinkin Dunia

Yahouza SadissouDecember 8, 2005

An shiga sa in sa tsakanin Majalisar Dinki Dunia da Erythrea sakamakon hunkuncin da Gwamnatin Asmara ta yanke na kora wasu ma´aikatan tawagar Majalisar.

https://p.dw.com/p/Bu3Y

A halin da ake ciki wata cacar baka ta kabre tsakanin Majalisar Dinkin Dunia, da gwamnatin kasar Erythrea.

Idan ba ku manta ba, ranar talata ne, gwamnatin ta hido sanarwar kora wasu ,daga jami´an malajalisar dinkin dunia,160 da su ka hada da, Amurika, Rashawa da Turawa, dake aikin sa iddo, domin aiki da yarjejeniyar zaman lahia, da a ka cimma tsakanin Ethiopia da Erythrea a shekara ta 2002 bayan shearu 2 na yake -yake.

Sanarwar ta ba wannan mutane, wa´adin kwanaki 10, na su fita daga kasar Erythrea.

Ba da wata wata ba, Majalisar Dinkin Dunia, ta maida martani inda ta ce sam, batun wani jami´in ta ,ya fita, bai ma taso ba.

Sakatare Janar na Majalisar, Koffi Annan ya yi tur da wannan aniya, ya kuma kiri gwamnatin Erythrea, da ta lashe amen ta.

Wani jami´in diplomatia, ya bayyana cewa Gwamnatin Asmara, ta dauki wannan mataki, domin a ganin ta, Majalisar Dinkin Dunia, na nuna san cuziyya, a cikin rikicin ,da ya hada Ethiopia da Eryhtrea.

Ranar 23 ga watan November da ya wuce,Komitin Sulhu ya sa hannu a kan dokar kashedi ga kasashen 2, da su daina shirye shiryen komawa fagen daga, idan kuma ba haka ba, komitin zai saka takunkumi, ga kasar da ta burjinewa umurnin.

A daya gefen,sanarwar komitin Sulhun, ta yi kanda, ga Erythrea, da ta yi watsi da hukuncin da ta yanke ,na hana jiragen samar majalisar Dinkin Dunia, shawagi a sararin samaniyar ta.

Gwamantin Erythrea, ta zargi Komitin Sulhu da rufe ido, ga matakin da Ethiopia ta dauka, na kin amincewa a shata iyaka, kamar yada komitin da ya jagorancin shiga tsakani ya tsara.

A nasa bangare, shugaban tawagar Majalisar Dinkin Dunia a kasashen Ethiopia da Erythrea,Jean marie Guehenno, ya kiri taron manema labarai,inda ya jaddada cewar, hakika, mutanen 160, da Gwamnatin Erythrea, ke bukatar kora, ba su zuwa ko koffa.

Kasar Ethiopia, ita ma, ta hurta albarkacin bakin ta, a cikin wannan cacar baka, inda ta yi Allah wadai, da daukar matakin, wanda ko shaka babu inji sanarwar zai kara, dagulla yunkurin cimma zaman lahia, a yankin.

A sahiyar yau, wani mai magana da yawun gwamnatin Eryhtrea, ya maida buda, ga bukatar Majalisar Dinkin Dunia.

Jami´in ya ce babu gudu, babu ja da baya, a game da shawara da gwamnati ta yanke, na kora wannan mutane, nan da kwanakin da aka yanke, masu.

Ya ce Eryhtrea, kasa ce mai cikkaken yanci , a game da haka, ba za ta taba yarda ba, wani ya zo daga wata dunia ya tsara mata abinda, ba zai wa yan kasa dadi ba.

Gwamnatin ba tare da matsin lamba,ba, ta amince da sa hannu a kan dokar da ta girka tawagar majalisar Dunia, a kasashen Erythrea da Habasha,kuma a cikin yancin da ke gare ta, ta yanke shawara kora wasu daga cikin ma´aikatan wannan tawaga,da bincike ya gano cewa,suna wuce gona da iri, kuma zaman su, ba alheri ba ne ga kasar.

To hausawa kan ce mai abu ya rantse mara abu ya rantse, yanzu sai a zuba iddo a yi kallo.