1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bush zai samu kyakyawar tarba a ziyarar da zai kai Albaniya

June 10, 2007
https://p.dw.com/p/BuJN
A yau shugaban Amirka GWB ya ke ziyara kasar Albaniya inda zai gana da shugaban kasa Moisiu da FM Berisha da kuma wakilan gwamnatocin Kuratiya da Macedoniya a Tirana babban birnin Albaniya. A ziyarar da ya kaiwa Italiya a jiya Bush ya gana da FM Romano Prodi a birnin Rom, bayan ya kaiwa paparoman Benedict na 16 ziyarar ban girma a fadar Vatikan. Paparoma ya yi amfani da wannan ziyara inda ya nuna damuwarsa game da halin da ake ciki a Iraqi. Sannan ya yi kira ga Bush da ya nemi hanyoyin diplomasiya don warware rikicin yankin GTT. An dai yi arangama tsakanin ´yan sanda da masu zanga-zangar nuna adawa da ziyarar ta Bush a birnin Rom. Akalla mutane dubu 150 suka yi maci a babban birnin na Italiya don yin tir da Bush da kuma yakin Iraqi.