Bush zai gana da Musharraf da Karzai | Labarai | DW | 27.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bush zai gana da Musharraf da Karzai

A yau shugaba Bush na Amurka yake ganawa da shugabannin kasashen Pakistan da Afghanistan wato Parvez Musharraf da Hamid Karzai,a kokarinsa sasanta tsakani bisa batun mayakan Taliban da shugabnin biyu suke zargin juna a kansu.

Karzai da Musharraf cikin makon daya gabata sunyi musayar yawu game da hanyoyin da kowannensu yake daukar batun yan Taliban dake bakin iyakokin kasashen biyu.

Kasar Afghanistan ta zargi Pakistan cewa,daga cikin kasar ne yan Taliban suke kai hare hare kasar Afghanistan,batu da shugaban Pakistan din ya Musharraf ya karyata.