1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bush zai gabatar sabbin takunkumi a kan gwamnatin Sudan

May 29, 2007
https://p.dw.com/p/BuKT

Shugaban Amurka George W Bush na shirin sanyawa Sudan sabbin takunkumi tare da kiran Majalisar ɗinkin duniya ta zartar da ƙudiri da zai tilastwa gwamnatin Sudan ɗin ta daina yin cikas ga yunƙurin ƙasa da ƙasa na kawo ƙarshen zubar da jini a Dafur. A ranar Talatan nan ake sa ran shugaba Bush zai baiyana sabbin matakan ladabtarwa a kan Sudan bisa Imanin da ya yi cewa halin da ake ciki a Dafur ya taázzara. Sabbin matakan za su tsaurara sharuɗan da aka sanyawa ƙasar tun da farko da kuma ƙarin wasu kamfanoni na ƙasar Sudan waɗanda zaá haramtawa yin amfani da kafofin kuɗaɗe na Amurka, da kuma dirar mikiya a kan wasu mutane waɗanda ke da hannu a rikicin Dafur da ya yi sanadiyar mutane fiye da 200,000 da kuma tilastawa wasu jamaár kimanin miliyan biyu da rabi yin ƙaura daga gidajen su shekaru huɗu da suka wuce. Bugu da ƙari shugaban ya kuma umarci sakatariyar harkokin wajen Amurka Condolezza Rice ta tsara daftari da zaá miƙawa majalisar ɗinkin duniya domin ɗaukar tsauraran matakan akan gwamnatin Sudan ta Omar al-Bashir.