1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bush yayi hannun ka mai sanda na ƙarshe ga Omar El Bashir

Shugaba Georges Bush na Amurika, ya bayyana yin hannun ka mai sanda, na ƙarshe ga hukumomin Sudan, a dangane da batun yankin Darfur.

Bush yayi kira ga shugaba Omar El Bashir, ya gaggauta amincewa, da karɓar dakarun shiga tsakani na Majalisar Ɗinkin Dunia, a wannan yanki da ke fama da tashe –tashen hankulla.

Idan kuma yayi kunnen uwar shegu, Amurika ba da ɓata lokaci ba, za ta ƙara tsuke takunkumin karya tattalin arzikin Sudan, da ma sauran wasu ƙarin matakai na ladabtarwa wanda shugaban mai bayyana ba.

Matakan karya tattalin arzikin ,sun shafi wasu kampanoni 29 mallakar ƙasar Sudan, wanda kwata-kwata za a haramtawa saye da sayarwa da Amurika.

A cikin jawabi mai tsauri, Bush ya gargaɗi Omar El Bashir, tare da cewar , Amurika ta gaji da ɗaukar renin hukumomin Khartum.

A nasa gefen, Praministan Britania Tony Blair, ya bayana cewar, gobe alhamis, Amurika da Engla, za su tanttana, domin ɓullo da wani saban ƙudurin da za su gabatarawa komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia a game da ƙasar Sudan.