1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bush yayi Allah wadai da tashin bom din nan da akayi a Jordan

Shugaba Bush na Amurka ya mika sakon ta´aziyyar sa ga shugaba Abdullah na Jordan, sakamakon tashin bama baman nan da suka yi asarar rayuka sama da hamsin a waje daya kuma da jikkata wasu sama da dari.

Shugaba Bush wanda ya mika ta´aziyyar tasa ta wayar tangaraho a lokacin da yake tattaunawa da shugaba Abdullah, a yau alhamis, a inda ya kara da cewa hakan ba zai girgizasu ba ko kadan dangane da kokarin da suke na yaki da aiyukan ta´addanci da kuma yan Ta´adda.

Ya zuwa yanzu dai kungiyyar nan ta Alqeeda da Abu Musab Alzarqawi kewa jagoranci a kasar iraqi ce tace ita keda alhakin kai wannan hari.

Kungiyyar ta Alzarqawi wanda Amurka ke nema ruwa a jallo ta fadi hakan ne kuwa a cikin wani sako data aike izuwa yanar giza gizan sadarwa na duniya wato Internet a turance.