1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bush yace babu gudu babu ja da baya a Iraqi

October 24, 2006
https://p.dw.com/p/Buen

Shugaban Amurka George W Bush yace babu gudu babu ja da baya a Iraqi a dangane da matsin lambar da gwamnatin sa ke fuskanta na sauyin dabaru a game da manufofin ta a Iraqi. Yayin da zaben Majalisun dokokin Amurkan ke kara gabatowa Bush na fuskantar matsanancin suka daga yan jamíyar Demokrats da gazawa wajen shawo kan tabarbarewar alámura a Iraqi. Shugaban na Amurka yace suna auna kokarin gwamnatin Iraqi a kan mizani wajen ganin cewa sojojin Iraqin sun sami cikakkiyar kwarewa da za su iya tafiyar da shaánin tsaron kasar. Rahotanni kuma daga Bagadaza na cewa wani sojin Amurka ya bace tun daren jiya har yanzu baá gano shi ba. Wasu bayanai na cewa sojin dan asalin Iraqi ne. Wani babban hafsan sojin Amurkan a birnin Washington yace jamiín na daga cikin rukunin sojoji masu aikin fassara, wasu bayanan kuma na cewa yan takife ne suka yi garkuwa da shi