1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bush ya sanar da aniyar rufe sansanin Guantanamo

June 21, 2006
https://p.dw.com/p/But0

Shugaban Amurka George W Bush yace zai rufe gidan yarin Guwantanamo dake sansanin sojin Amurka a Cuba. Bush ya furta hakan ne a yayin taron koli tsakanin Amurka da kungiyar tarayyar turai wanda ya gudana a birnin Vienna na kasar Austria. Da yake maida martani ga bukatar kungiyar tarayyar turai na rufe gidan yarin na Guantanamo, Bush yace yana sauraron bayanai ne daga kotun kolin Amurka kan yadda zaá yiwa mutanen da ake tsare da su a wannan sansani bisa ayyukan taáddanci shariá. Yace ya fahimci damuwar kasashen turai, Bush ya kara da cewa zaá mayar da wadanda ake tsare da su zuwa kasashen su na asali, to amma yace akwai wadanda ya kamata a yi wa shariá a kotunan Amurka. Wolfang Schüssel Shugaban Gwamnatin Austria wadda ke rike da shugabancin karba karba na kungiyar tarayyar turai yace sansanin Guantanamo ya haifar da matukar damuwa ta fuskar shariá.