1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bush ya musanta yunkurin kaiwa Iran farmaki

April 10, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2Q

Shugaban Amurka George W Bush yace jita jita ne kawai rahotannin da kafofin yada labarai suke bayarwa cewa Amurka na shirin kaiwa kasar Iran farmaki. Yana mai cewa tafarkin hani shine hada hannu wuri guda domin ganin Iran ba ta mallaki makamin kare dangi ba. Bush yace sun sha jin bayanai dake nuni da cewa idan washington taki amincewa da abu, to ana nufin zata yi amfani da karfin soji, yana mai cewa a wannan matakin magana ce ta fuskar diplomasiya. A nasa bangaren shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmedinejad yace babu gudu babu ja da baya a game da shirin kasar sa na makamin nukiliya. Ahmedinejad ya kuma sa kafa ya yi fatali da bukatar kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya na dakatar da shirin sa na sarrafa sinadarin Uranium. A jawabin da ya yiwa alúmar kasar, Mahmoud Ahmedinejad yatabbatar musu da cewa ba zai ba da kai bori ya hau ba wadanda ya baiyana da cewa makiyan kasar Iran ne.