Bush ya kwantanta halin da ake ciki a Iraki da wanda aka fuskanta a yakin Vietnam | Labarai | DW | 19.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bush ya kwantanta halin da ake ciki a Iraki da wanda aka fuskanta a yakin Vietnam

A dangane da asarar sojoji da Amirka ke kara yi kullum a Iraqi, a karon farko shugaba GWB ya amsa cewa ana iya kwatanta karuwar tashe tashen hankula a Iraqi da yakin Vietnam. Bush ya ce hare haren da masu ta da kayar baya na Islama ke kaiwa a Iraqin sun yi kama da na yakin sunkurun Vietnam na shekarar 1968, wanda ya sa ala tilas aka kawo karshen wannan yaki a wancan lokaci. A Iraqin dai a cikin sa´o´i 24 kacal, an kashe sojojin Amirka 11, wato kasar ta yi asarar sojoji 69 a cikin makonni biyu na watannan na oktoba. Majiyoyin ma´aikatar tsaron Amirka sun ce ana duba yiwuwar sake komawa da wata bataliya ta sojojin wucin gadin kasar zuwa Iraqi.