1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bush ya kammala ziyararsa a Turai

June 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuJB

A karshen ziyararsa zuwa turai,a kasar Bulgaria shugaban Amurka G Bush ya yaba da sauye sauyen tsarin kasuwanci na tsohuwar kasat ta kominist.

Bayan tattaunawarsa da shugaban Bulgarian Georgi Parvanov,Bush yace damuwar da kasar ta Bulagrai take yi game da kafa tashar kare makamai masu linzami a nahiyar turai bashi da tushe.

Bush yace yana neman kyakyawar hulda da Rasha.

Amurkan dai tana bukatar wannan tasha ta rika kare abinda ta kira barazana na harin makamai masu linzami daga kasashe kamar su Iran da Koriya ta arewa.

Bush ya kuma roki kasar Libya data saki maaikatan jiyya nan 5 yan kasar Bulagaria wadanda suke fuskanatr hukuncin kisa,bayan an zarge su da yiwa yaran kasar 426 alllurar kwayar cutar AIDS.