Bush ya jinkirta sanarwar sauyin salo a Iraqi
December 14, 2006Talla
Shugaban Amurka George W Bush yace ba zai yi gaggawar yin garanbawul ga manufofin Amurka a Iraqi ba. Hakan dai ya biyo bayan shawarar da ya yanke ne ta jinkirta sanarwa a game da sabbin manufofin ya zuwa sabuwar shekara. Shugaban na cigaba da tattaunawa da tare da neman shawarwari daga manyan jamián Amurka dana Iraqi. A wani taron manema labarai, shugaba Bush wanda ke fuskantar matsin lamba ya sauya salo a Iraqi, ya yi alfahari da cewa sojin ƙawance da Amurka kewa jagoranci ta kashe abokan gaba kimanin 5,900 a ciki da wajen Iraqi a watanni uku da suka gabata.