Bush ya jaddada goyon baya ga P/M Iraqi Nuri al-Maliki | Labarai | DW | 17.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bush ya jaddada goyon baya ga P/M Iraqi Nuri al-Maliki

Shugaban Amurka George W Bush ya jaddada goyon bayan sa ga P/M Iraqi Nuri al-Maliki, yayin da a waje guda kuma ya kare gwamnatin sa daga kiraye kirayen da ake mata na sanya waádin lokaci na ficewar sojin Amurka daga ƙasar Iraqi. Kakakin fadar white House Tony Snow yace Bush fayyacewa P/M Nuri al-Maliki sabanin fahimtar cewa Amurka ta bashi watanni biyu domin shawo kan tarzomar dake faruwa a ƙasar. Yana mai cewa waɗannan raɗe raɗi ba gaskiya bane kuma Amurka na bashi cikakken goyon baya. Waɗannan bayanai dai sun biyo bayan kiran da wani ɗan majalisar dattijan Amurka John Warner ya yi ne cewa ya kamata Amurka ta sake salon tunani idan rikicin Iraqin ya cigaba da wanzuwa har tsawon watanni biyu zuwa uku nan gaba. Warner wanda har ila yau shi ne shugaban kwamitin soji na majalisar dattijan, a cikin wannan watan ya dawo daga Iraqi inda ya baiyana cewa babu wani cigaba da gwamnatin ta al-Mailiki ta yi na shawo kan alámura a Iraqi. Ƙasar Iraqi na cigaba da fuskantar tarzoma inda tashin bama bamai a Bagadaza da wasu sassa na ƙasar ke hallaka rayuwar jamaá da dama.