Bush ya hau kujerar na ƙi a kan dokar kuɗi ga yaƙin Iraqi | Labarai | DW | 02.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bush ya hau kujerar na ƙi a kan dokar kuɗi ga yaƙin Iraqi

Shugaban Amurka George W Bush ya hau kujerar naƙi a kan ƙudirin samar da kuɗi don tafiyar da yaƙin Iraqi wanda yan majalisar dokoki suka jingina da waádin janye sojoji a cikin watan Oktoba. Bayan ƙin sanya hannu a kan ƙudirin shugaba Bush ya kuma shaidawa alúmar Amurka cewa yan Demokrats za su jefa kwamandojin sojin cikin mawuyacin hali idan aka amince da sanya waádin lokaci na ficewar sojojin daga ƙasar Iraqi, yana mai cewa hakan zai zama tamkar miƙa wuya ne ga abokan gaba. Da take maida martani kakakin majalisar dokokin tarayya Nancy Pelocy tace labbuda majalisar ba zata sakarwa Bush wuka da Nama ya kashe kuɗaɗe yadda yake so domin cigaba da yakin Iraqin ba.