1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bush ya gana da Paparoma Benedikt na 16

June 9, 2007
https://p.dw.com/p/BuJS

An yi ganawar farko tsakanin shugaban ƙasar Amurika Georges Bush da shugaban ɗarikar roman katolika ta dunia, Paparoma Benedikt na 16.

Mahimman batutuwan da su ka tanttana akai, sun haɗa da rikicin gabas ta tsakiya, da kuma sakamakon taron ƙungiyar G8, da aka kammala jiya a birnin Heiligendamm na ƙasar Jamus.

A game da taron G8, Paparoma ya nuna gamsuwa, da nasara da shugabanin su ka cimma , mussamman taimakon dala milion dubu 60, da ƙasashen masu ƙarfin tattalin arziki su ka alkawarta baiwa Afrika, domin ta yaƙi cuttutukan Aids, malaria da tarin huka.

A dangane da rikicin gabas ta tsakiya, Paparoma ya buƙaci maida fifiko, wajen samar da zaman lahia mai ɗorewa, ta hanyar tsoma bakin ƙasashen yakin,cikin kwanciyar hankali da fahintar juna.