1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bush ya ce yana iya bijirewa majalisu don aiwatar da manufarsa a Iraqi

January 13, 2007
https://p.dw.com/p/BuUZ

Shugaban Amirka GWB ya ce zai dage kan shirin sa na tura karin sojoji sama da dubu 20 zuwa Iraqi, ko da kuwa ´yan majalisun dokoki sun yi mwatsi da wannan shiri. Bush ya fadawa gidan telebijin na CBS cewa yana iya bijirewa majalisun dokokin, don ya tabbatar da sabbin manufofin sa da nufin kawo karshen tashe tashen hankula a Iraqi sun samu nasara.

“´Ya´yan majalisar na da ´yancin bayyana ra´ayoyinsu. To amma wadanda suka ki bawa wannan shirin damar don yayi nasara, to suna da alhakin gabatar da wani shiri na dabam wanda ke da kyakkyawar alamar yin nasara. Nuna adawa da wani abu ba tare da an gabatar da wani a madadinsa ba rashin sanin ciwon kai ne.”