1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bush ya ce shi ya ba da umarnin yiwa Amirkawa leken asiri

December 17, 2005
https://p.dw.com/p/BvG1

Shugaban Amirka GWB ya amsa cewar shi ya ba da wani umarni na sirri bayan hare haren ta´adancin 11 ga watan satumban shekara ta 2001, wanda ya ba damar sauraron hirarrakin ´yan kasar ba tare da izinin kotu ba. A cikin jawabin sa na mako mako da yake yiwa Amirkawa ta radiyo, Bush ya ce daukar wannan mataki yana da muhimmanci don kare al´umar kasar ta Amirka daga ayyukan ´yan ta´adda. Da farko dai jaridar New York Times ta ba da labarin wannan umarni da shugaban ya bayar. A jiya juma´a gwamnatin shugaba Bush ta fuskanci babban koma-baya bayan da majalisar dattawa ta ki amincewa da sabunta dokar tabbatar da kishin kasa, wadda ta kasance kashin bayan yaki da ta´addanci da shugaban ya kaddamar. A daura da haka ´yan majalisar sun kara matsa kaimi ne a bukatunsu na inganta dokokin tsaron lafiyar jama´a.