1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bush ya ce Amirka ba zata gaggauta janye dakarun ta daga Iraki ba

December 9, 2006
https://p.dw.com/p/BuYa

Shugaban Amirka GWB ya sake yin watsi da duk wani shirin janye dakarun Amirka cikin gaggawa daga Iraqi. A cikin jawabin sa na mako mako Bush ya ce hukumar nan ta Baker ta nunar da cewa yin haka zai tsananta rikicin da ake yi tsakanin mabiya addinai daban daban a Iraqi. Haka kuwa zai kara jefa al´umar kasar cikin mawuyacin hali fiye da wanda suke ciki a yanzu. Ya ce kafin bukin kirismati fadar White House zata gabatar da sabuwar alkiblar da zata dauka.

Insert O-Ton Bush:

“Gwamnati na nazarin shawarwarin da rahoton Baker ya gabatar. A lokaci daya kuma ma´aikatun tsaro da na harkokin waje da kuma majalisar tsaron kasa na dab da kammala aikinsu game da manufonfinmu a Iraqi. Ina sa ido don ganin na su shawarwari kafin in yanke shawara.”