Bush ya baiyana rashin gamsuwa da gwamnatin Iraqi ta Nuri al-Maliki | Labarai | DW | 22.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bush ya baiyana rashin gamsuwa da gwamnatin Iraqi ta Nuri al-Maliki

Shugaban Amurka George W Bush ya baiyana rashin gamsuwa da gwamnatin Iraqi ƙarkashin jagorancin P/M Nuri al-Maliki. Bush yayi wannan furucin ne a wani taro na shugabanin arewacin Amurka da ya gudana a Montebello a Canada. Shima jakadan Amurka a Iraqi Ryan Crocker ya soki lamirin gwamnatin Iraqin da gazawa wajen shawo kan tarzomar dake faruwa da kuma sasanta kan alúmar ƙasar. Crocker wanda ke bin diddigin alámura a Iraqin domin tattara bayanai gabanin rahoton da zai gabatar ga majalisar dokokin Amurka yace babu wani cigaban azo a gani da mahukuntan na Bagadaza suka yi wajen sasanta ɓagarori da basa ga maciji da juna, yana mai cewa akwai iyaka ga irin goyon bayan da Amurka ke baiwa gwamnatin ta P/M Nuri al-Maliki. A waje ɗaya kuma Ministan harkokin wajen Faransa Bernard Kouchner yace wajibi ne tarayyar turai bada gagarumar gudunmawa a Iraqi domin Amurka ita kaɗai ba zata iya fidda Iraqi daga matsalolin da ta faɗa ciki ba. Kouchner shine jamiín gwamnatin Faransa na farko da ya ziyarci ƙasar Iraqin tun bayan mamayen sojojin ƙawance da Amurka ta jagoranta domin kifar da gwamnatin Saddam Hussaini a shekarar 2003.