Bush ya bada umurnin dakatar da kadarorin masu yiwa gwamnatin Lebanon zagon kasa | Labarai | DW | 02.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bush ya bada umurnin dakatar da kadarorin masu yiwa gwamnatin Lebanon zagon kasa

Shugaba Bush na Amurka ya bada umurnin a dakatar da dukkanin kadarorin wadanda Amurkan take ganin suke zagon kasa ga gwamnatin kasar Lebanon.

Kodayake Bush bai baiyana sunayen wadannan mutane ba amma a watan yuni ya kafa dokar hana shiga kasar Amurkan ga wasu jamian kasar Syria da yan siyasa na Lebanon wadanda gwamnatin Amurkan take zargi da tada zaune tsaye a kasar ta Lebanon.

Bush yace wannan umurni ya shafi dukkan masu kawo cikas ga gwamnatin Lebanon da kuma masu tsoma baki na kasar Syria wadanda zaa dakatar da kadarorin da suke da su a kasar Amurka.