1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bush na fuskantar matsin lamba a game da yaƙin Irak

April 3, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3F

Gwamnatin shugaba Georges Bush na Amurika na ƙarin fuskantar matsin lamba daga ciki da wajen ƙasar a game da yaƙin ƙasar Irak.

A ranar jiya, Janar mai ritaya Anthony Zinni, wanda ya jagoranci rundunar sojojin Amurika tsakanin shekara ta 1997 zuwa 2000 a yankin Golf ya bukaci sakataran tsaro na Amurika Donald Rumsfeld yayi murabus, saboda kura- kurai, masu yawa da ya tabka, a game da yaƙin ƙasar Iraki.

Wannan babban jami´in soja, mai kwarjini a Amurika, ya bayyana ɓacin rai, a kan rashin sannin makamar aiki, na sakataran harakokin tsaron ƙasar.

Jannar Zinni ,ya yi kira ga shugaba Bush da ya manta, da duk wata, alaƙa ko amintaka, da ta haɗa shi, da Donald Rumsfeld, ya sauke shi daga wannan matsayi, wanda akan sa, ya nuna kasawa mattuƙa.

A ɗaya hannu kuma, a cen ƙasar Irakin, an gano gawwakin matuƙa jirgin samar Amurika mai durra angullu, da wasu yan ƙunar baƙin wake sun ka kakkabo ranar assabar da ta wuce.