1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bush na ƙoƙarin samun goyon Jamus ga manufofin harkokin wajen gwamnatinsa

Kwanaki kaɗan bayan dawowar shugabar gwamnatin tarayyar Jamus Angela Merkel, daga ziyarar da ta kai a birnin Washington a makon da ya gabata ne, kafofin yaɗa labaran Jamus suka buga wata fira da suka yi da shugaba Bush, inda yake nanata cewa ya manta da batun saɓannin da aka samu tsakanin ƙasashen biyu dangane da yaƙin Iraqi. To ko mece ce manufarsa takamaimai ?

Bush da Angela Merkel a lokacin da ta kai masa ziyara a fadar White House.

Bush da Angela Merkel a lokacin da ta kai masa ziyara a fadar White House.

A nan Jamus dai, kafofin yaɗa labarai sun yi ta yabon ziyarar da shugaban gwamnatin tarayya Angela Merkel ta kai a makon da ya gabata abirnin Washington. Bisa dukkan alamu dai, shugaban na Amirkay a fi jituwa da shugaba Merkel da tsohon shugaba Gerhard Schröder. Ana iya ganin hakan, idan aka yi la’akari da dogon lokacin da shugabannin biyu suka shafe suna tattaunawa, da amsa gayyatar Angela Merkel zuwa nan Jamus da shubaban na Amirkay a yi ko kuma nasarar da shugaban ta Jamus ta samu wajen gayyatar ’yan kasuwar Amirka zuba jari a nan Jamus.

A ɓangare ɗaya dai, ana nanata irin ƙoƙarin da shugaban ta Jamus ke yi ne wajen sake farfaɗo da kwarjinin Jamus a Amirka. A ɗaya ɓangaren, kafofin yaɗa labaran na ganin Bush tamkar nema yake yi kawai na samun goyon bayan Jamus ga manufofinta na ƙetare. Don cim ma wannan burin ne kawai ba don komai ba, ya sa shugaban na Amirka ya amince da yin fira da kafofin yaɗa labaran Jamus. Sabili da haka ne ya ce ya manta da saɓanin da aka samu tsakanin ƙasashen biyu game da yaƙin Iraqi.

A halin yanzu dai, ba batun Iraqin ne ya fi ci wa shugaban na Amirka tuwo a ƙwarya ba, tun da dakarunsa na girke a can. Game da Iran kuwa, yana bukatar goyon baya, kafin ya iya yi wa Jumhuriyar Islaman katsalandan. Ya dai rasa samun irin wannan goyon bayan a Rasha da kuma Sin. Sabili da haka ne kuwa, kwatsam, ba zato ba tsammani Washington ta fara zargin Moscow da rashin bin tafarkin dimukraɗiyya, wai kamar yadda ya kamata. Duk da nanatawar da yake ta yi ta cewa suna tuntuɓar juna da shugaba Putin a ko yaushe, shugaba Bush dai bai cim ma nasarar shawo kan takwaran aikinsa na Rashan ya goyi bayan manufofinsa a kan wannan batun ba.

Daga ɓangaren Angela Merkel, shugaban gwamnatin tarayyar Jamus kuwa, shugaba Bush ya sami tabbacin cewa Jamus a shirye take ta bi sahun Amirka a kan wannan batun na rikici da Iran.

A bainar jama’a dai, Amirka da muƙarrabanta na ta nnanata cewa, suna sha’awar ganin an warware wannan matsalar ta hanyar diplomasiyya. Sai dai sanin kowa ne, abin da ita Amirkan ke nufi a nan shi ne duk mai adawa da fadar White House, to ya kamata ya saduda. Idan ko ya ƙi miƙa wuya, kamar yadda Iran ke yi a halin yanzu, to Amirka za ta iya afka masa da ƙarfin soji.

Abin tambaya a nan shi ne, wai shin da gaske Jamus take ala kulli halin ta mara wa Amirka baya a kan wannan batun ? Ko wa ke farin ciki a nan Jamus da abin da yake gani kamar sassauucin tsamari tsakanin ƙasar da Amirka, to kamata ya yi ya san cewa, miƙa hannun da shugaba Bush ke yi ba alama ce ta lumana ko kuma hannunka mai sanda ba. Neman abokan burmi kawai shugaban ke yi a lokacin da yake bukatansu. Idan kuma ya cim ma burinsa, sai ya yi watsi da su.

 • Kwanan wata 08.05.2006
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu0J
 • Kwanan wata 08.05.2006
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu0J