1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bush a yankin Gabas ta tsakiya

Karshen ziyarar Bush a gabas ta tsakiya

default

George Bush da Sarki Abdallah

A yau ne dai shugaban na Amirka George W Bush zai kai ziyara Masar wadda ke zama zangon ƙarshe na ziyarar mako guda da ya kai ƙasashen yankin gabas ta tsakiya. Sai dai kuma tuni jamiýun adawa ciki har da Muslim Brothers da kungiyoyin kare cigaban dimokradiyya suka fara zanga zangar rashin amanna da ziyarar ta Bush zuwa Masar. Gamal Zahran na jamíyar Independa ya baiyana zuwan na Bush da cewa ziyara ce wadda bata da wani amfani. A jiya Talata dai shugaban na Amirka George W Bush ya gana da Sarki Abdalla na Saudiyya inda ya sami kyakyawar tarba. Wannan dai ita ce ziyara ta farko da shugaba Bush ya kai ziyara zuwa ƙasar Saudiyya tun bayan da ya hau karagar mulki. ya

Shugabanin biyu sun tattauna akan muhimman batutuwa da suka haɗa da halin da ake ciki na farashin ɗanyen mai, wanda hakan ya sa shugaban na Amirka ya nemi taimakon ƙasar Saudiyya wajen sassauta tashin gwauron zabi farashin man. Hauhawar farashin man a cewar Bush zai shafi tattalin arzikin Amirka. A saboda haka yace yana fata ƙungiyar ƙasashe masu arzikin mai a duniya OPEC za ta ƙara yawan man da ƙasashen ke haƙowa, yace hakan zai taimaka matuƙa wajen sassauta farashin.

Sauran batutuwan da Bush ya tattauna da Sarki Abdallah na Saudiya sun haɗa da batun zaman lafiya tsakanin Israila da Falasɗinawa.

Sai dai a yayin da ake ƙoƙarin ɗinke ɓaraka tsakanin Yahudawan da Falasɗinawa, a jiya Israila ta kai hari Gaza wanda ya hallaka Falasɗinawa goma sha tara da jikata wasu da dama. Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas ya yi tur da Allah wadai da wannan hari