Burundi: Yunkurin wanzar da zaman lafiya | Siyasa | DW | 08.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Burundi: Yunkurin wanzar da zaman lafiya

Mai shiga tsakanin na Kungiyar Tarayyar Afirka a rikicin kasar Burundi Benjamin Mkapa ya isa birnin Bujumbura don da maido bangarorin da ke hamayya da juna a kasar kan tebirin tattaunawa.

Tun a yammacin jiya Larabar da ta gabata ce tsohon shugaban Tanzaniya Benjamin Mkapa ya isa birnin Bujumbura don tattaunawa da wanda suke da ruwa da tsaki a wanna harka ta zaman sulhu tsakanin wanda ba sa ga maciji da juna. Sai dai kuma ga dukkan alamu zai yi wuya yinkurin mai shiga tsakanin ya yi tasiri domin tuni bangaren adawa a karkashin kawancan Cnared ya fito fili ya bayyana rashin amincewarsa da shi a bisa zarginsa da kasancewa mai kusanci da shugaba Nkurunziza.

'Yan adawar kasar ta Burundi na kuma zargi mai shiga tsakanin da kasa tabuka komi  na ci gaba a batun sansanta rikicin kasar tun bayan da aka nada shi. Sai dai mai shiga tsakanin ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba kuma a shirye ya ke ya tattauna da wakillan 'yan adawar da ke zaman gudun hijira a ketare kafin sake kiran wani zaman taron. To amma kuma yaduwar kashe-kashen gilla da ake yi wa 'yan adawa da ma wasu na kusa da shugaban kasa na mayar da hannun agogo baya ga duk wani yinkuri da ake na shawo kan rikicin kasar.

Sai dai gwamnatin kasar ta Burundi a yanzu haka na ci gaba da kasancewa kan matsayinta na sai an maido da zaman tattaunawar a cikin kasa kuma ba za ta amince ta tattauna da wakillan 'yan adawa da ke zaman gudun hijira ba. Mai shiga tsakani na tarayyar Afirka a rikicin kasar ta Burundi na da burin kai bangarorin siyasar kasar ga cimma yarjejeniya nan da watan Yulin shekarar badi ta 2017.

Sauti da bidiyo akan labarin