1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burundi: Soke kungiyar kare hakin dan Adam ta Iteka

Salissou Boukari
January 3, 2017

Ofishin ministan cikin gidan kasar Burundi ya fitar da wani kudiri da ya soke kungiyar Iteka da ke a matsayin kungiyar kare hakin dan Adam mafi dadewa a kasar.

https://p.dw.com/p/2VCRR
Afrika Wahl in Burundi Tote bei Protesten
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

Wannan kungiya ta Iteka da ke nufin diyauci a harshen Kirundi na kasar ta Burundi, an kafata ne tun a shekara ta 1991, kuma aka dakatar da ita tun farkon rikicin siyasar da ya barke a watan Afrilu na 2015,  lokacin da Shugaba Pierre Nkurunziza ya sanar da aniyarsa ta sake tsawa takarar neman shugabncin kasar ta Burundi a lokacin da ake kallon cewa wa'adin mulkinsa ya kawo karshe.

Wannan mataki dai ya biyo bayan wani rahoto da kungiyar ta fitar tare da hadin gwiwar kungiyar kare hakin dan Adam ta duniya da kungiyar ta Iteka ke wakilta a kasar ta Burundi, kan iri-irin cin zarafin da ke gudana a kasar. Sai dai hukumomin na Burundin na zargin wannan kungiya da ci gaba da bata sunan kasar a idanun duniya.