1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin zaben raba gardama a Burundi

Salissou Boukari
May 15, 2018

A ranar Alhamis da ke tafe 'yan kasar Burundi ke kada kuri'a a zaben raba gardama wanda zai bai wa shugaban kasar Pierre Nkurunziza damar ci gaba da mulki har zuwa shekarar 2034.

https://p.dw.com/p/2xm3h
Burundi Gitega -  President Pierre Nkurunziza  bei Wahlkampaqne
Shugaba Nkurunziza na Burundi yayin yakin neman zabeHoto: E. Ngendakumana

'Yan Burundi kimanin miliyan hudu da dubu dari takwas ne za su yi zaben kwatankwacin kashi 40 cikin 100 na al'ummar kasar da suka yi rajista, inda za su zabi amincewa ko kuma akasin haka da sauye-sauyen kudin tsarin mulkin kasar.

Tun bayan da Shugaban Nkurunziza ya sake tsayawa takara mai cike da cece kuce a shekarar 2015 wanda ake kallo a matsayin wani wa'adin mulki na uku, lamarin ya jefa kasar ta Burundi cikin tashe-tashen hankula da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 1, 200 yayin da wasu sama da dubu 400 suka kasance 'yan gudun hijira.