Burma ta kara yawan wadanda ta tsare | Labarai | DW | 17.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Burma ta kara yawan wadanda ta tsare

Gwamnatin mulkin soja ta kasar Burma ta kara yawan mutane da tace ta tsare tun farko a zangazangar kin amincewa da gwamnati da aka gudanar.Gwamnatin ta maida martani ne saboda matsin lamba da take samu daga kasashen duniya inda tace ta tsare akalla mutane 3,000 maimakon 2,100 da ta baiyana tun farko.Gidan TV na kasar ya bada rahoton cewa har yanzu mutane 500 suna tsare,bayan rikicin daya halaka mutane 13,cikinsu har da wani dan jarida na kasar Japan daya daga cikin kasashe dake baiwa Burma gudumowa,kasar ta japan a yanzu ta soke taimakon dala miliyan 5 da ta yi niyyar baiwa Burma tun farko.