1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso: Sojoji sun fatataki 'yan ta'adda

Salissou Boukari
November 10, 2017

Wata majiyar ma'aikatar tsaro daga Ouagadougou a Burkina Faso ta ce Sojoji masu sintiri na kasar sun hallaka wasu 'yan ta'adda guda hudu tare da karbe tarin makammai daga 'yan ta'addan a yankin Ariel iyaka da Mali.

https://p.dw.com/p/2nOXC
Burkina Faso Militär Soldaten Symbolbild
Sojoji masu sintiri a Burkina FasoHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Wani babban sojan kasar ta Burkina Faso ya sanar da wannan labari, inda ya ce sojojinsu biyar sun samu raunuka kuma daya daga cikinsu na cikin mawuyacin hali. Sojojin na Burkina Faso sun samu kwato makammai masu yawa da alburusai daga hannun maharan. Arewacin kasar ta Burkina Faso dai mai makwabtaka da kasar Mali da kuma Jamhuriyar Nijar, na fama da tarin matsalolin tsaro, inda wani adadi da hukumomin kasar suka bayar a farkon shekara ta 2015 ya nuna cewa 'yan jihadin sun kai hari har sau 80 da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 133 daga wannan lokaci zuwa farkon watan Nuwamba na 2017