Burkina Faso: Ceto jarirai daga HIV | Sauyi a Afirka | DW | 29.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Sauyi a Afirka

Burkina Faso: Ceto jarirai daga HIV

Wata mata na amfani da basirarta wajen kare yaduwar cutar HIV daga uwa zuwa jarirai da ke yawaita a Burkina Faso.

Cutar HIV mai karya garkuwar jiki dai na cikin manyan matsalolin da ke kisan kananan yara a duniya, wanda kuwa suke dauka ta hanyar shan nono uwa da ma lokacin haihuwa.

Kimanin mata 30 da ke zaune a wata cibiya da aka tanadar musamman a Burkina Faso na fama ne da larura guda, wato suna dauke da kwayar cutar HIV mai karya garkuwar jiki. Matan dai basu son a bayyana sunayensu.

Sai dai Rachel Yameogo da ke dauke da cutar shekaru 24 a yanzu, ta bambanta da wadannan matan na farko, don tana ma son duniya ta san halin da take ciki na kasancewa da cutar ta HIV.

Tana aiki da wata kungiyar taimaka wa masu fama da larurar cutar, kuma tun a shekarar 2004 take bai wa matan da ke dauke da cutar kuma ke da juna biyu shawarwarin yadda za su haifu ba tare da cutar ta sami jariransu ba.

Kusanm mutane dubu 110 ne dai ke dauke da kwayar wannan cutar a kasar Burkina Faso, kuma dubu 13 yara ne kanana da aka haifa da ita.

DW Webvideo Burkina Faso (DW)

Rachel Yameogo ta kungiyar Aide-moi à être mère a Burkina Faso

Rachel Yameogo ta ce ana iya kare kamuwar jarirai.

"Idan iyaye mata da ke dauke da cutar suka rika samun maganin rage kaifinta, zai rage hadarin bai wa yaron da ke ciki matuka."

Taimako daga gwamnati don rage kaifin HIV

Gwamnatin kasar Burkina Faso dai na bayar da maganin rage kaifin HIV kyauta ga wadanda ke fama da larurar, sai dai mata masu yawa basa yarda a yi masu gwaji, saboda gudun kyama, inji Yameogo.

"Idan aka sami mace da kwayar cutar, tilas mu tallafa mata saboda galibi irinsu, muna ganin danginsu na watsi da su saboda cutar. Yawanci mutane ba su fahimci matsalar ba."

Wannan mata Rachel Yameogo da ke jagorantar kungiyar da ta kafa tana samun nasarori a aikin da take yi na fadakar da mata masu fama da larurar ta HIV.

Südafrika Impfung gegen Tuberkulose Archiv 2011 (AFP/Getty Images/Rodger Bosch)

Kula da kiwon lafiyar yara manyan gobe

Wannan mata mai dauke da juna biyu, cewa ta yi "ina son in kula da ciki na, in san ko ina dauke da wannan cuta don in kama magani."

In kunne ya ji jiki ya tsira

Wannan shiri dai na ikirarin samun nasara ga musamman iyayen da suka bi umarnin masana, yara kuma na samun tsira daga cutar.

Cuta mai karya garkuwar jikin dai na ci gaba da zama babbar matsala saboda karancin yadda ake magana a kanta kamar sauran wasu matsaloli na lafiya tsakanin jama'a.

Wata matashiya da bata son a bayyana ta, ta bayyana yadda rayuwar danta karami nan-gaba ke damunta.

"Bayan haihuwarsa, ba zan iya bashi magani ba, saboda ina fargabar kada uwar miji na ta san ina tare da wannan cutar."

Alkaluma sun nunar da cewa, kokarin wannan matar Rachel Yameogo a Burkina Faso, ya taimaka wa mata kimanin 1300 da a yanzu ke da lafiyayyun yaran da basu kamu da cutar ba.

A bayyane yake dai Hukumar Lafiya ta Duniya na bukatar irin wadannan kungiyoyi don cikar burin nan nata na yaki da cutar HIV nan da shekara ta 2030 a duniya.