Burin Wyclef Jean na zama shugaban Haiti
August 6, 2010Wyclef Jean, shaharraen mawaƙin hip-hop a ƙasar Amirka ya ba da sanarwar niyyarsa ta tsayawa takararar zaɓen shugaban Haiti, wadda ƙasa ce da talauci yayi wa katutu da kuma har yanzu take fama da raɗaɗin bala'in girgizar ƙasa da ta rutsa da ita a watan Janairun wannan shekara. Mawaƙin, wanda ya ci kyautar fice ta Grammy har sau uku, ya ba da sanarwar haka ne a wani taron magoya bayansa da ya gudana a Port-au-Prince babban birnin ƙasar ta Haiti. A cikin wata fira ta musamman da CNN ta yi da shi, ya nuna dalilinsa na shiga wannan takara. Ko shakka babu Jean wanda tsohon mamba ne na ƙungiyar mawaƙar Fugees zai jefa kansa a cikin takara mai sarƙaƙƙiyar gaske, da kuma aiki mai haɗari. Mutun ɗaya ne dai kaɗai ya taɓa kammala wa'adin shugabancinsa na shekaru biyar a tarihin ƙasar ta Haiti.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu