1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

burin MDD dangane da shekara ta 2015

May 24, 2005

Har yau ana fama da tafiyar hawainiya a kokarin kayyade matsalar talauci da yunwa nan da shekara ta 2015

https://p.dw.com/p/Bvbi

A cikin rahoton nasu kungiyoyin taimakon daga kasashe shida na Turai, abin da ya hada har da kungiyar taimakon abinci ta Jamus Welthungerhilfe, sun yi nuni da cewar ko da yake kasashen Kungiyar Tarayyar Turai ba su yi sako-sako da manufar ba, inda suke ba da taimako mai tsoka a fafutukar kayyade matsaloli na talauci da yunwa a dukkan sassa na duniya, amma fa har yau da sauran rina a kaba. An saurara daga bakin Hans-Joachim Preuß, sakatare-janar na kungiyar Welthungerhilfe yana mai bayanin cewar:

Ba shakka kungiyar tarayyar Turai ta tashi haikan wajen daukar nagartattun matakai akan manufa kuma wasu daga cikin kasashenta sun kara yawan taimakon da suka saba bayarwa, amma fa a daya bangaren akwai masu yi wa lamarin rikon sakainar kashi, daga cikinsu kuwa har da Jamus, wacce ke nuni da gibin kasafin kudinta tamkar abin dake hana ruwa gudu. Amma fa lamarin gaba daya ya danganta ne da niyyar mutum. Muddin kasashen Turai na fatan samun fada a ji a siyasar duniya to kuwa tilas ne su kara karfafa rawar da suke takawa a dangantakun kasa da kasa.

Rahoton gamayyar kungiyoyin taimakon masu zaman kansu, wanda aka gabatar da shi a jiya litinin a nan birnin Bonn yana bincike ne akan bangarorin da ya kamata a mayar da hankali kansu domin cimma burin na shekara ta 2015, kamar dai yaki da jahilci da manufofin kiwon lafiya. Kazalika rahoton ya nazarci tasirin dukkan shirye-shiryen da aka gabatar a kasashen da lamarin ya shafa a wawware. A lokacin da take bayani kakakin gamayyar mai taken Alliance 2015, Marion Aberle cewa tayi babbar manufarsu shi ne bin diddigin dukkan matakan da ake dauka daga bangaren kasashe masu tasowa da kuma bangaren kasashen KTT dake ba da taimakon. Domin kuwa sau tari zaka tarar ana cika baki wajen yin alkawurrukan taimako ba tare da an cika su ba. Dangane da kudurin na MDD, ba kawai maganar yawan taimakon ne ke da muhimmanci ba, kazalika hanyoyin aiwatar da shi. Kafin wata kasar dake ba da taimako ta cancanci yabo wajibi ne ya kasance taimakon da take bayarwa yana da nufin yaki ne da matsalar talauci da jahilci da kuma kyautata kiwon lafiya kai tsaye. Daga cikin kasashen da suka cancanci yabo dangane da rawar da suke takawa wajen ba da taimakon domin cimma burin na MDD dangane da shekarata 2015 har da Irland da Denmark da kuma Holland, a yayinda gaggan kasashen KTT kamar Jamus aka baro su can baya. Wani abin lura a nan ma shi ne kasashe masu tasowan kansu sun fi taka rawar gani a kokarin cimma burin na kayyade talauci da yunwa akan kasashe masu ci gaban masana’antu dake da wadatar arziki.