Bunkasar Sojan Haya a Iraki | Siyasa | DW | 26.04.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bunkasar Sojan Haya a Iraki

Yawan sojojin haya sai dada karuwa yake yi a kasar Iraki, nda aka kiyasce adadinsu ya kai dubu 15 zuwa dubu 25. Wato ke nan su ne rukunin soja mafi yawa a baya ga dakarun sojan Amurka a Iraki

Tabarbarewar tsaro a Iraki

Tabarbarewar tsaro a Iraki

Har yau dai ana ci gaba da kai ruwa rana dangane da ragowar Italiyawa su uku da ake garkuwa da su a kasar Iraki. Dangane da takwaransu Fabrizio Quattrochi kuwa tuni bakin alkalami ya bushe, saboda masu garkuwa da shi sun bindige shi har lahira misalin makonni biyu da suka wuce. Fabrizio Quattrochi, wanda ya bakunci lahira yana da shekaru 36 da haifuwa jami’in tsaro ne na wani kamfanin tsaro na Amurka dake zaman kansa kuma ya kasance yana da dangantaka ta kut-da-kut da uwar kungiyoyin kamfanonin tsaro masu zaman kansu ta duniya Ibssa a takaice, wacce ke da mazauninta a Budapest, kamar yadda aka ji daga shugaban gamayyar George Popper lokacin hira da tashar Deutsche Welle. Ta kan wannan gamayyar ce Fabrizio ya samu horo a matsayin mai tsaron lafiya, sai dai kuma ba wanda ya san tahakikanin abin da ya kai shi kasar iraki tare da takwarorin nasa su uku. Rahotanni sun ce an dora musu alhakin tsaron wani otel ne a birnin Bagadaza. Amma abin dake akwa shi ne kasancewar tuni kasar Iraki ta zama wani dandali dake da cunkoson kamfanonin tsaro masu zaman kansu, ko kuma sojan haya a takaice, kamar yadda aka ji daga bakin Enrique Bernales Ballesteros, wakilin MDD akan al’amuran sojan haya, wanda kuma ya kara da bayyana damuwarsa da wannan ci gaba da ake samu a kasar Iraki. Jami’in, wanda tun abin da ya kama daga shekarar 1987 ne yake bin diddigin al’amuran sojan haya da sunan MDD yayi nuni da cewar:

"Wannan ci gaba ne dake da ban tsaro saboda kokarin da ake yi na danka alhakin yakin a hannun kamfanonin tsaro masu zaman kansu. A nan ana iya batu a game da wani sabon yanayi na vaikin sojan haya da aka shiga. Domin kuwa, wadannan sojojin sun saba da mayaka ‚yan kasada da aka saba gani a yake-yaken neman ‚yancin kan kasashen Afurka. A nan batu ake yi a game da wani mummunan yanayi mai hadarin gaske ga makomar kasashen da lamarin ya shafa."

A halin yanzu haka wadannan sojojin haya sune suka fi yawa a baya ga sojojin Amurka a kasar Iraki, inda ake batu a game da dakarun mayaka dubu 15 zuwa dubu 25 na sojan hanyar. Da yawa daga kamfanonin na adawa da wannan tambari na sojan haya da ake yi musu, kamar yadda shi kansa George Popper, shugaban gamayyar Ibssa ya nunar, inda kuma ya kara da cewar:

"Kamfanonin tsaro masu zaman kansu ba zasu iya mayewa gurbin soja ba. Kazalika ba sa daukar nauyin tafiyar da matakan kwantar da tarzoma ko wani mataki na kundumbala. Alhakin da ya rataya wuyansu shi ne ba da horar da mutane game da kare kafofi ko gidaje ko mutane ko kuma wajen jigilar takardun kudi da makamantansu. Wani muhimmin abu game da horon shi ne yadda mutum zai iya gane ‚yan ta’adda ya kuma yakesu."

A dai halin da ake ciki yanzu kasar Iraki na neman maza makabartar wadannan sojojin haya, inda ake yawaita garkuwa da kuma kisansu, kamar yadda ya wakana akan wasu ‚yan Amurka su hudu a Falujja karshen watan maris da ya wuce. Kasashen Amurka da Birtaniya dai sun lashi takobin mayar da bangaren dakarun soja a hannun kamfanoni masu zaman kansu, inda Amurkan take kashe kashi 10% na kasafin kundinta na tsaro wajen mara wa kamfanonin tsaro masu zaman kansu baya.