Bundestag za ta yi muhawara kan tura dakarun Jamus zuwa Kongo. | Labarai | DW | 17.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bundestag za ta yi muhawara kan tura dakarun Jamus zuwa Kongo.

A yau ne Majalisar Dokokin Jamus ta Bundestag, za ta yanke shawara kan amincewa ko kuma yin watsi da batun tura dakarun ƙasar zuwa Jumhuriyar Dimukraɗiyya Ta Kwango, ƙarƙashin wani shirin da Ƙungiyar Haɗin Kan Turai ta sanya a gaba, na tura dakarun kare zaman lafiya zuwa wannan ƙasa, a lokacin zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar a ran 30 ga watan Yuli.

Ana kyautata zaton cewa, ministan tsaro na tarayya, Franz Josef Jung, zai gabatar wa Majalisar tsarinsa, na ba da gudummowar dakaru ɗari 8 ga rundunar ta EU.

A farkon wannan makon ne dai, Ƙungiyar EUn ta ba da sanarwar cewa, a mataki na farko, za ta girke dakaru ɗari 4 da 50 ne a cikin kasar ta Kwango. Sa’annan kuma, za ta ajiye wani rukunin da ya ƙunshi dakaru dubu ɗaya, a ƙasashe masu maƙwabtaka da Kwangon, waɗanda za su yi katsalandan a Kwango ne kawai, idan Majalisar Ɗinkin Duniya ta bukace su da yin hakan.