Bundestag tayi mahawara akan KTT | Siyasa | DW | 16.06.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bundestag tayi mahawara akan KTT

A zamanta na yau alhamis majalisar dokokin Jamus Bundestag tayi mahawara akan halin da kungiyar tarayyar Turai ke ciki dangane da matsaloli na kudi da daftarin tsarin mulki bai daya tsakanin kasashenta

Gerhard Schröder na jawabi ga majalisar dokoki ta Bundestag

Gerhard Schröder na jawabi ga majalisar dokoki ta Bundestag

A karon farko a zauren mahawarar ta majalisar dokokin Bundestag shugabar jam’iyyar CDU Angela Merkel tayi jawabi a matsayin babbar ‚yar takarar jam’iyyun Christian Union dake neman mukamin shugaban gwamnatin Jamus, inda tayi suka da kakkausan harshe a game da kai ruwa ranar da ake famar yi dangane da makomar kungiyar tarayyar Turai. A nasa bangaren shugaban gwamnatin Jamus, ko da yake ya bayyana takaicinsa a game da halin da ake ciki sakamakon fatali da daftarin tsarin mulkin kungiyar da aka yi a kasashen Faransa da Netherlands, amma ya yi kira da a ci gaba da sanya albarka akan kundin, inda yake cewar:

Kasashe goma ne suka albarkaci daftarin tsarin mulkin, abin da ya hada har da Jamus. Akwai kuma wasu da suka ce zasu yi hakan nan ba da dadewa ba. A saboda haka babatun da ake yi a majalisar Turai, inda wasu ke cewar wai maganar daftarin tsarin mulkin ta sha ruwa, wannan babban kuskure ne dake taimakawa wajen zubar da martabar kungiyar a idanun jama’a.

Schröder ya ba da shawarar cewar wajibi ne a danka lamarin a hannun kwamitin ministocin KTT a kuma ci gaba da manufar karbar karin kasashe a kungiyar duk da matsalolin da ake fama da su yanzu haka. Wannan ba lokaci ba ne da ya kamata a sake mayar da hannun agogo baya. Kamata yayi a karbi kasashen Rumaniya da Bulgariya sannan a shiga shawarwarin karbar kasar Turkiyya a kungiyar ta tarayyar Turai in ji Schröder. A nata bangaren Angela Merkel, babbar ‚yar takarar jam’iyyun Christian Union tayi gargadi a game da neman wuce gona da iri a matakan karbar karin kasashe a kungiyar tarayyar Turai. ‚Yan Christian Union ba sa kaunar ganin an karbi Turkiyya, illa kawai a kulla wata yarjejeniya ta kawance da ita. A ganinta kin amincewa da daftarin tsarin mulkin kungiyar da aka yi a kasashen Faransa da Netherlands abu ne dake bayyana irin fargabar dake tattare a zukatan jama’a a kasashen kungiyar tarayyar Turai, wanda kuma ya kamata a ba da la’akari da shi sosai da sosai a taron kolin shuagabannin kasashen da za a fara a yammacin yau alhamis a birnin Brussels. Dangane da rikicin kasafin kudin da ake famar kai ruwa rana kansa kuwa, Schröder yayi nuni ne da cewar Jamus bata da ikon yin kari akan gudmmawar da ta saba bayarwa, ko da yake a shirye take ta ga an cimma wata manufa mai sassauci a tsakani. Kazalika yana fatan ganin Birtaniya ta nuna halin sanin ya kamata bisa manufa. Domin kuwa babu wani dalili na ci gaba da yi wa Birtaniyar alfarmar da tayi sama da shekaru 20 tana samu na rangwamen gudummawar da take bayarwa ga baitul-malin kungiyar ta tarayyar Turai. To sai dai kuma shugaban gwamnatin na Jamus ya nuna tababarsa a game da yiwuwar cimma daidaituwa akan wannan matsalar a zauren taron kolin daga yau alhamis zuwa gobe juma’a idan Allah Ya kai mu.