Bundesliga Radio kai tsaye | Zamantakewa | DW | 26.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Bundesliga Radio kai tsaye

A daidai lokacin da ake shiga kakar wasannin kwallon kafa ta lig-lig na kasar Jamus wato Bundesliga, yanzu haka masu sauraron tashar rediyon DW na iya sauraron wadannan wasanni kai tsaye ta akwatunansu na rediyo.

Tun daga ranar Asabar 27 ga watan Augustan shekara 2016 muka fara gabatar da wadannan wasanni kai tsaye ta harsunan Hausa da Suwahili. A cewar kwararren mai gabatar da sharhi kan harkokin wasannin motsa jiki na sashen Hausa na DW Umaru Aliyu "Wannan tamkar mafarki ne ya zama zahiri."

Tsawon lokaci kenan tashoshin rediyoyin Afirka da ke hulda damu ke muradin ganin an fara gabatar da wasannin kwallon kafar na Bundesliga kai tsaye kamar yadda BBC ke yi a lokacin da ake buga wasannin Premier League. Tun daga ranar 27 ga watan Augusta, dama ta samu ga miliyoyin masu sauraron wannan tasha ta DW da ke Yammaci da Gabashin Afirka.

Gasar wasannin Bundesliga kai tsaye

Kai tsaye ma'aikatanmu za su rika gabatar muku da sharhi cikin harsunan Hausa da Suwahili na guda daga cikin wasannin da suka fi kayatarwa a ko wacce Asabar da rana kai tsaye, tare da hadin kan kwararru a fannin wasannin kwallon kafa na tashar DW.

Umaru Aliyu

Umaru Aliyu, kwararren mai gabatar da sharhi kan harkokin wasannin motsa jiki na sashen Hausa na DW

A cewar shugaban sashen Afirka Claus Stäcker "Afirka nahiya ce da al'ummarta ke kaunar wasannin kwallon kafa. Kuma masoyan kwallon kafan sun san sunayen kusan kowa da ke buga kwallo a tawagar kwallon kafar Jamus da ta sha zama zakara a harkokin wasanni a duniya."

Sunaye kamar "Schweinsteiger, Özil da Joachim Löw" dai, sun kasance a leben masoya wasannin Afirka tun bayan da Jamus ta lashe gasar cin kofin kwallon kafa na duniya. Bajintar 'yan wasan kwallon kafar na Jamus dai da irin salonsu na buga kwallo da ma yadda suke jefa kwallo a cikin raga ya dauki hankalin jama'a.

Wasannin Bundesliga a ranakun Asabar

Saurari sauti

Za ku iya sauraron shirin na wasannin Bundesligar kai tsaye da misalin karfe uku da minti 25 agogon Najeriya, Nijar Kamaru da Chadi, wato karfe biyu da minti 25 agogon GMT da Ghana, ta hanyar gajeren zango kan mitoci 16 | 17840 kHz da mitoci 19 | 15195 kHz

Za ku ma a iya sauraronmu kai tsaye ta shafinmu na intanet lokacin da ake wasan ko kuma a tashoshin abokanan huldar DW da ke a yankunanku a wadannan kasashe:

Najeriya:

Freedom Radio – Kano, Dutse, Kaduna

Prestige FM - Minna

Rima FM 97.1 – Sokoto

Liberty FM – Kaduna

BRC – Bauchi

Progress Radio – Gombe

Radio Gotel – Yola

Unity FM – Jos

 

Nijar:

Alternative - Niamey

Anfani – Niamey, Diffa, Maradi, Zinder

Dallol - Baleyara, Dogondoutchi, Matankari, Tchibiri

Tambara - Tahoua

Garkuwa – Maradi

Fara'a - Dioundiou, Dosso, Gaya

Hadin Kay - Aguié, Dakoro, Magaria, Tagriss

Murya Talaka Filingué – Filingué

Niyya – Konni

Nomade - Agadez

Saraounia - Madaoua, Maradi, Tahoua

Shukurah – Zinder

Tarmamuwa – Tessaoua

Té Bon Sé - Tillabéri

Radio Rurale de Rounkondoum- Doumega

 

Ghana

Justice FM - Tamale

Zuria FM – Kumasi

 

Kamaru

Radio Communautaire Tikiri FM - Meiganga

Radio Salaaman  - Garoua

 

Burkina Faso:

Horizon FM - Fada-Ngourma

Côte d'Ivoire:

Tere FM – Abidjan

 

Mali:

Koukia FM 107.8 - Ansongo

Radio Rurale - Ménaka

Radio Voix des Foghass - Bourem

 

Senegal:

Radio Dunyaa FM – Tamba