1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bunƙasar ƙungiyoyin farar hula

Mutane na daɗa dawowa daga rakiyar jam'iyyun siyasa a sassa daban-daban na duniya

default

Ƙungiyoyin farar hula kan shiga zanga-zanga don neman buƙatunsu

A yayinda jami'iyyun siyasa da ƙungiyoyin ƙwadago ke kokawa game da asarar membobi da suke yi, a ɗaya ɓangaren kuma ana samun ƙaruwar mutanen dake shiga zanga-zanga, ba a ƙarƙashin tutar wata ƙungiya ba. Wannan maganar ba kawai ta shafi Jamus kaɗai ba ne har ma da sauran ƙasashe, inda mutane ba su da cikakkiyar amanna da 'yan siyasa, a maimakon haka suke ba da ƙarfi ga ƙungiyoyin farar hula.

"A shekarar da ta wuce, sannan ina can ƙasar Argentina, na jefa ƙuri'a ta ne ta hanyar wasiƙa a zaɓen majalisar dokokin da aka gudanar, saboda muhimmancin wannan zaɓe gare ni. Amma kuma ta zanga-zanga ni da sauran takwarorina muke iya bayyana ainihin alƙiblar da muka fuskanta."

Wannan bayanin an ji shi ne daga bakin wani matashi da ake kira Fabio dake da shekara 20 da haifuwa. Fabio dake zaune a birnin Kolon yayi aikin bauta wa ƙasa na tsawon shekara ɗaya a ƙetare kuma a halin yanzu yana karatu ne a jami'ar Bonn kuma yana sha'awar al'amuran siyasa. Tun yana da shekaru 16 da haifuwa yake halartar zanga-zanga idan har ta shafi wani lamari ne dake da muhimmanci a gare shi. Ya shiga zanga-zangar adawa da wariyar jinsi da ƙyamar baƙi da zazzafar aƙidar mazan-jiya da ma wasu manufofin na siyasa. Misali dai ƙara wa'adin aikin tashoshin makamashin nukiliya ko tsuke bakin aljihun gwamnati a al'amuran ilimi. A ganinsa ba za a iya cimma buƙatun siyasa a demoƙraɗiyyance a ƙarƙashin jam'iyyun siyasa ba. Kuma ko da yake Fabio na ci gaba da shiga zaɓe, amma ba ya da ra'ayin cewar jam'iyyun siyasar, alal-haƙiƙa, suna wakiltar buƙatunsa ne. Irin wannan ci gaba kuwa ba kawai ya shafi Jamus ne kaɗai ba. A sassa daban-daban na duniya a halin yanzu haka zaka tarar da dubban ɗaruruwan mutane dake haɗe kansu ƙarƙashin wata ƙungiya ta farar hula a maimakon shiga inuwar wata jam'iyya ta siyasa. Wannan aƙidar ta cewar siyasa bata jiɓantar maslahar al'uma sai daɗa yaɗuwa take yi, kazalika da ma maganar cewar demoƙraɗiyya ba kawai ta shafi jefa ƙuri'a ba ne. Christina Figueres, shugabar sakatariyar Majalisar Ɗinkin Duniya akan yanayi tayi marhaban da wannan ci gaba inda take cewar:

"Abin madalla shi ne yadda ƙungiyoyin farar hula suka shiga ana damawa da su a mahawarar da ake yi akan canje-canjen yanayi. A taron Majalisar Ɗinkin Duniya akan yanayin da aka gudanar a Kopenhagen shekarar da ta wuce, mun samu halarcin wakilan ƙungiyoyin farar hula fiye da zamanin baya kuma muna sauraron halartarsu a taron da za a yi a Cacun watan desamba mai zuwa."

Greenpeace Banner Klimagipfel Kopenhagen

Ƙungiyar Greenpeace a Kopenhagen

An lura da irin wannan ci gaba a matakin tsayar da ranar yaƙi da yunwa da talauci a shekarar da ta wuce, in ji Evelin Herfkens, tsofuwar ministar taimakon raya ƙasashe masu tasowa ta ƙasar Netherlands, wadda kuma a halin yanzu take haɗa kan matakan cimma burin nan na ƙarni. Ta dai yi bayani tana mai cewar:

"A ganina mun cimma ƙolulowa a fafutukar kai wa ga burin nan na ƙarni, inda a watan oktoban bara mutane sama da miliyan 173 a sassa daban-daban na duniya suka tsaya suna masu kira ga gwamnatocinsu da su ba da gudummawa wajen ganin an cimma wannan buri."

A halin yanzun dai tambayar dake akwai ita ce ta yaya za a raya makomar demoƙraɗiyya a wannan ƙari na 21 da duniya ke daɗa kusantar juna. Tuni dai ƙungiyoyin farar hula suka zama ruwan dare a duniyar, amma siyasa sai ci gaba da lalube take yi a cikin duhu don neman alƙiblar da zata fuskanta.

Mawallafi: Helle Jeppesen/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi