Bullar murar tsuntsaye a Jamus | Labarai | DW | 15.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bullar murar tsuntsaye a Jamus

Hukumomin kula da lafiya anan Jamus,sun bada tabbacin cewa,agwagin ruwa guda 2 da aka samu sun mace a kasar,suna dauke da kwayar cutar masassarar tsuntsaye ta H5N1.

Cibiyar kula da kare yaduwar cututtuka ta Robert Koch a nan Jamus,ta baiyana cewa babu shakka kwayar cutar ce ta kashe wadannan agwagi a tsibirin Rügen.

Yanzu haka an umurci dukkan masu kiwon kaji da su killace dabbobinsu daga ranar jumaa.

Ministan kula da lafiya na Jamus,Horst Seehofer ya shawarci masu kiwon kajin da su gaggauta kare kajin nasu ba tare da bata lokaci ba.

Wannan mataki dai ya biyo bayan samun kwayar cutar ce a jikin tsuntsaye a kasashen Girka da Italiya,hakazalika kasar Austria ta bada rahoton samun kwayar cutar a jikin wasu tsuntsaye da suka mutu.