1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bullar masu dauke da kwaryar cutar H5N1 a Turkiyya

January 9, 2006
https://p.dw.com/p/BvD4

Ma´aikatar kula da lafiya ta kasar Turkiyya ta bayar da sanarwar mutane biyar da suke dauke da kwayar cutar murar tsuntsaye.

Ya zuwa yanzu dai mutanen dake dauke da wannan cuta a cewar ma´aikatar lafiya ta kasar sun kai mutane 14, ciki har da mutum biyu da suka rasa rayukan su.

Idan dai an tuna koda a makon daya gabata, sai da wasu mutane uku yan gida daya suka rasa rayukan su, sakamakon kamuwa da wannan cuta mai nau´in H5N1.

Faruwar wannan sabon abu dai ya haifar da gudanar da taron gaggawa na kwararru a wannan fanni da suka fito daga hukumar lafiya ta duniya , wanda yanzu haka ke gudana a kasar ta Turkiyya.

Tuni dai mahukuntan kungiyyar Eu suka hana shigo da gashin dabbobi da a kalailaice lafiyar sa ba izuwa mambobin kasashen ta, daga kasashe shida da suka yi iyaka da kasar ta Turkiyya.

ka rasa rayukan su a makon daya gabata.