Bullar masassarar tsuntsaye a Birtaniya da Kuratiya | Labarai | DW | 22.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bullar masassarar tsuntsaye a Birtaniya da Kuratiya

An ba da rahoton bullar matsananciyar murar tsuntsaye a kasashen Birtaniya da kuma Kuratiya. A halin da ake ciki hukumomin Birtaniya sun rike wani aku da aka shiga da shi kasar daga Surinam, kuma yanzu haka an kai shi da wasu tsuntsaye da aka fito da su daga Taiwan wani kebebben wuri da ba shiga ba fita. To sai dai har yanzu ba´a tabbatar ba ko tsuntsaye sun kamu da nau´in cutar ta H5N1 dake da hadari ga dan Adam. A halin da ake ciki KTT na shirin kafa dokar haramta shigo da kaji da dangogin su daga kasar Kuratiya. Rahotanni sun ce a ranar litinin mai zuwa ake sa ran dokar zata fara aiki. A nan Jamus kuwa tun daga yau dokar killace kaji da tsuntsaye ta fara aiki.