Bullar cutar murar tsuntsaye a Turkiyya | Labarai | DW | 05.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bullar cutar murar tsuntsaye a Turkiyya

Jami´an kiwon lafiya a kasar Turkiyya sun shaidar da rasuwar wani matashi guda a kasar sakamakon kamuwa da yayi da cutar murar tsuntsaye.

Hakan kuwa ya biyo bayan gano wadansu mutane biyu ne dauke da kwayar cutar ta murar tsuntsaye a gabashin kasar ta Turkiyya.

Rahotanni dai sun nunar da cewa wannan al´amari na a matsayin abu na farko ne dake da nasaba da mutuwar mutane a wajen kasashen yankin Asia, wanda keda alaka da cutar murar tsuntsayen.

Daga dai shekara ta 2003 zuwa yanzu an kiyasta cewa wannan cuta ta murar tsuntsaye tayi aja.lin mutane sama da 70 a wasu kasashe na gabashin Asia, banda kuma miliyoyin tsuntsaye da aka halaka a matsayin riga kafi, wanda hausawa kance yafi magani.