Bullar cutar murar tsuntsaye a Turkiyya | Siyasa | DW | 05.01.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bullar cutar murar tsuntsaye a Turkiyya

Bullar kwayoyin cutar zazzabin murar tsuntsaye ya kashe yara biyu daga gida guda a Turkiyya,wanda shine ke zama karo na farkon bullar wannan cuta a jikin biladama a wajen kasar Sin da kasashen dake yankin kudu maso gabashin Asia.

Duk dacewa babu matabbaciya sosai a dangane da kwayoyin cutar da ake kira H5Ni,mutuwar matasan biyu na nuni da cewa wannan zazzabin murar tsuntsaye ya doshi nahiyar turai,cutar data kashe mutane 74 a gabashin asia da bullar ta a shekarata 2003.

Yaran biyu dai sun fit one daga wani kauye dake kan iyakar Turkiyya da Armenia ta gabashi,inda kuma mutane ke rayuwa wuri guda da dabbobin dake da nasaba da tsuntsaye,wadanda suke kiwo domin abinci.

Gwamnan gunduwar Van, Niyazi Tanilir ya sanarwa manema labarai cewa bayan rasuwar mehmet Ali Kocyigit mai shekaru 14 da haihuwa a karshen mako,yar uwarsa Fatma Kocyigit mai shekaru 15 da haihuwa ta rasu da safiyar yau.

Kafofin yada labaran yankin dai sun yayata hotunan binne Mehmet a jiya laraba,inda aka tona kabari mai zurfi da kumayin amfani da lemon tsami a matsayin kari akan kabarin nasa.

Jamiar lafiya na Turkiyyan dai sun danganta rasuwar wannan matashi da zazzabin murar tsuntsayen.An tabbatar da hakan ne sakamakon bincike da aka gudanar a asibitoci biyu kan kwayoyin wannan cuta.Mai bada shawara na musamman kan cututtuka dake yaduwa a ofishin turai na hukumar kula da lafiya ta mdd Guenael Rodier ya tabbatar dacewa wannan zazzabin murar tsuntsayen ne ya bulla a jikin biladama.

A hiran da akayi dashi ta wayan tangaraho daga Copenhagen ,jamiin yace ana bukatar kara yin wasu gwaje gwaje domin hakikancve cewa kwayoyin cutar ta H5NI din ne ya sake bayyana kuma yayi sanadiyar mutuwan wadannan yara biyu.

Gwamman gunduwar Van din dai ya sanar dacewa ayanzu haka akwai daya daga cikin iyalin marigayan dake cikin hali matsananci na jiya.

Duk dacewa wannan kwayar cutar na wahalar kamuwa da ita musamman daga tsuntsayen zuwa biladama,akwai barazanar kasancewar zuwa watata cuta da zata iya yaduwa cikin gaggawa a tsakanin biladama.Kwararru dai sun bayyana cewa idan hakan ya kasance zaayi asarar millioyoyin rayuka a duniya tare da durkushewar tattalin arziki.

Akan hakane wani jamming mdd yace labarin na turkiyya abun damuwa ne ,amma kada ya kasance abun razana.Dr David Nabarro na mdd yace a halin yanzu babu matsala,cutar zata fara yin barazana ne idan har aka fara samun yaduwarta tsakanin mutane.

 • Kwanan wata 05.01.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu2g
 • Kwanan wata 05.01.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu2g