Bullar cutar murar tsuntsaye a jamus | Labarai | DW | 06.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bullar cutar murar tsuntsaye a jamus

Hukumar kula da lafiyan dabbobi ta kasa ta sanar da bullar cutar murar tsuntsaye mai nauin H5N1,a tsakanin gonakin kajin gida anan jamus,bayan kashe wasu manyan tsuntsaye dake dauke da kwayyoin cutar.An gano cutar a jikin agwagwa ne a wata karamar gona dake kusa da birnin Wickersdorf dake jihar Thuerngen,inda ake kiwon agwagi guda biyar dasu kanan tsuntsaye.Tuni dai mai gonan ya kashe dukkanninsu.Wannan shine karo na farko da wannan cuta ta bulla ajikin tsuntsun gida a cikin wannan shekara a fadin tarayyar jamus,wadda kuma takan kama mutun har ta hallaka shi.Hukumomin kula da lafiyan jamus din dai na zargin cewa tsuntsayen sun fito ne daga Janhuriyasr Czech dake makwabtaka.