1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bulgariya na tattaunawa akan kafa asusun taimakon yaran Libya

January 21, 2006
https://p.dw.com/p/BvBF

Bulgariya na ci-gaba da tattaunawa da Libya akan kafa wani asusun taimakawa iyalan kananan yara da suka kamu da kwayoyin HIV a Libya. To sai dai har yanzu ba´a bayyana yawan kudin da za´a zuba cikin wannan asusu ba. Ana sa rai wannan asudu zai taimaka a rage kace-nace da ake yi dangane da ma´aikatan jiya su biyar na Bulgariya da kuma wani likita Bafalasdine da aka same su da laifin yiwa yaran allurar kwaoyin cutar HIV a Libya. Iyayen yaran dai na son a ba su diyya da ta kai Euro miliyan dubu 4.3, to amma Bulgariya ta ki hakan tana mai cewa ma´aikatan jiyyan ba su da laifin kamuwa da HIV da yaran suka yi. A na sa ran sake yin shari´ar mutanen 6 nan da wata daya.